explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labari cewa kowanne Musulmi ne ya karanta harafi daga littafin Allah, to, yana da lada a wannan karatun, kuma za a ninka masa lada zuwa ninki goma. Sannan ya yi bayanin hakan da faɗinsa: Ban ce : Alif, Laam, Meem, harafi ba ne, sai dai Alifun harafi ne, Lamun harafi ne, Mimun harafi ne, sai ya kasance harufa uku, lada talatin kenan.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa a kan yawaita karatun Alkur’ani.
  • Mai karatu a kowanne harafi na kalma da yake rerawa yana da lada da za’a nunka sau goma.
  • Yalwatuwar rahamar Allah, da kuma karamcinSa, ta yadda ya nunka wa bayinSa lada; falala ce da karamci daga gareShi.
  • Falalar Alƙur’ani a kan wani zancen da ba shi ba, da yadda ake bauta da karanta shi, saboda shi zancen Allah ne.