Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa

Daga Abu Hurairah Allah Ya yarda da shi, Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: Kada ku mayar da gidajenku makabarta, Shaiɗan yana guduwa daga gidan da ake karanta Surat Al-Bakarah a cikinsa".
Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana yin hani daga wofintar da gidaje daga sallah, sai su zama kamar maƙabartu, da ba a sallah a cikinsu. Sannan sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ba da labarin shaiɗan yana ficewa daga gidan da ake karanta Suratul Baƙara.

  1. Ana so a yawaita ibada da Sallolin Nafila a gidaje.
  2. Ba ya halatta yin Sallah a maƙabarta, domin hakan hanya ce daga hanyoyin shirka da wuce iyaka ga masu su, in banda sallar Janaza.
  3. Hanin yin Sallah a inda akwai kabari, ya tabbata a wurin Sahabbai, saboda haka Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya hana a sanya gidaje kamar maƙabartu, waɗanda su ba a Sallah a cikinsu.

An aika shi cikin Nasara