Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan dawwama kan karatun Alƙur'ani; domin shi (Alkur’ani) zai yi ceto a ranar alƙiyama ga masu karanta shi masu aiki da shi, sannan ya ƙarfafa karanta surori biyu: Baƙara da al-Imran, kuma ya ambace su da Zahrawani masu haske; saboda haskensu da kuma shiryarawarsu, kuma lallai ladan karanta su da tadabburin ma'anoninsu da kuma aiki da abinda ke cikinsu, zasu zo ranar alƙiyama kamar gizagizai biyu ko wasunsu, ko ka ce su garken tsntsaye ne waɗanda suka shinfiɗa fukafukansu sashinsu na saduwa da sashi, suna yi wa ma'abocinsu inuwa kuma suna kare shi. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa dawwama a kan karanta Suratul Baƙara da tadabburin ma'anoninta da kuma aiki da abinda ke cikinsu, kuma hakan a cikinsa akwai albarka da amfani mai girma a duniya da lahira, kuma barin hakan a cikinsa akwai asara da nadama a ranar alƙiyama, kuma daga cikin falalar wannan surar matsafa ba zasu iya cutar da wanda ya karantata ba.