Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Mu'azu Dan Jabal zuwa garuruwan Yaman yana mai kira zuwa ga Allah kuma mai ilimantarwa, ya bayyana masa cewa shi zai fuskanci wasu mutane daga Nasara; dan ya zama akan yi musu tanadi, sannan ya fara da mafi muhimmaci sannan mafi muhimmanci a kiran nasu, Sai ya kirasu zuwa gyara akida a farko; da cewa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne; Domin cewa da ita ne za su shiga Musulunci, idan sunyi imani da hakan sai ya umarcesu da tsaida sallah' domin cewa ita ce mafi girman wajibai bayan Tauhidi. Idan sun tsaida ita sai ya umarci mawadatan su da bada zakkar dukiyoyin su zuwa talakawansu, sannan ya gargade shi daga karbar mafificiyar dukiya; domin cewa wajibi shi ne tsaka-tsakiya, Sannan yayi masa wasicci da nisantar zalinci' dan kada wanda aka zalinta yayi masa mummunar addu'a domin cewa addu'arsa abar karbace.