Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana girman falalar Allah akan muminai, da kuma adalcinSa ga kafirai. Amma mumini ba za’a tauye ladan kyakkyawan da ya aikata ba; kai za'a ba shi ladan kyakkyawa anan duniya akan biyayyarsa, tare da abinda aka tanadar masa na sakayya a lahira; zai iya rabauta da kykkyawa gaba dayansa a lahira. Amma kafiri sai Allah Ya ba shi sakamakon abinda ya aikata na kyakkyawa da kyakkyawan duniya, har idan ya tafi lahira ba shi da wani ladan da za’a yi masa sakayya da shi a lahira; domin aiki na gari wanda zai yi anfani a duniya da lahira ba makawa mai shi sai ya zama mumini.