Manzo - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa Allah Ya ƙaddara kyawawa da munana, sannan Ya bayyanawa Mala'iku biyu yaya zasu rubuta su: Wanda ya yi nufin ya aikata kykkyawa za'a rubuta masa kyakkyawa ɗaya ko da bai aikatashi ba, idan ya aikatashi, to, za a ninkashi da tamkarsa goma zuwa ninki ɗari bakwai, zuwa ninki da yawa, ƙarin yana kasancewa ne da gwargwadan abin da ke cikin zuciya na ikhlasi da ƙetarewar amfani da makamancin hakan. Wanda ya yi nufin aikata mummuna sannan ya barshi saboda Allah, za a rubuta masa kykkyawa, idan ya barshi don shagaltuwa da barinsa, tare da rashin aikata sabubbanta ba za a rubuta masa komai ba, idan ya barshi don gajiyawa daga gareshi za a rubuta masa niyyarsa, idan ya aikatata za a rubuta masa mummuna ɗaya.