Daga Dalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Wani mutum daga cikin mutanen Najad ya zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - gashinsa ya yi datti, kuma muryarsa mai ƙarfi, ba'a fahimtar abinda yake faɗa, har ya kusanto ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi tambaya game da farillan musulunci? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara da sallah, kuma ya sanar da shi cewa Allah Ya faralanta masa salloli biyar a cikin kowanne yini da dare. Sai ya ce: Shin wani abu daga salloli sun wajaba a kaina banda waɗannan biyar ɗin? Sai ya ce: A'a, sai dai idan ka yi nafila daga sallolin nafila. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Daga abinda Allah Ya wajabta shi akanka azumin watan Ramadan. Sai mutumin ya ce: Shin akwai wani abu na azimi da ya wajaba a kaina banda azimin Ramadan? Sai ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila da wani azimi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ambata masa zakka. Sai mutumin ya ce: Shin wani abu na sadaka bayan farillar zakka ya wajaba a kaina? Ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila. Bayan mutumin ya ji waɗannan bayanai daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya juya baya ya yi rantsuwa da Allah - Maɗaukakin sarki - cewa shi zai dawwama a kansu ba tare da ƙari ko ragi ba, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce bayan haka: Idan ya gasgata abinda ya faɗa akan abinda ya rantse akansa to shi zai zama daga masu rabauta.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Saukin shari’ar musulunci da sauƙinta akan wadanda aka dorawa ita.
  • Kyakkyawan mu'amalarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wannan mutumin, haƙiƙa ya ba shi damar zuwa kusa da shi da kuma tambayarsa.
  • Farawa a cikin Da’awah zuwa ga Allah - Maɗaukkain sarki - da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci.
  • Musulunci aƙida ne da aiki, ba wani aiki da zai yi amfani ba tare da imani ba, kuma imani ba ya amfani ba tare da aiki ba.
  • Muhimmancin waɗannan ayyukan kuma cewa su suna daga rukunan musulunci.
  • Sallar Juma'a tana shiga cikin salloli biyar na wajibai; domin ita Juma’a canji ce daga sallar azahar ɗin ranar Juma'a ga wanda ta wajaba akansa.
  • Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara koyar da shi mafi ƙarfin farillan musulunci su ne rukunansa bayan kalamar shahada; domin shi ya kasance musulmi ne, bai ambaci hajji ba; domin shi kafin a wajabta shi ne, ko kuma shi lokacinsa bai zo ba.
  • Idan mutum ya taƙaita akan wajibi a cikin shari'a to shi ya rabauta, sai dai wannan ba ya nufin ba'a sunnanta masa ya zo da nafila ba; domin nafila farillai suna cika da ita ne a ranar AlKiyama.