Mikdadu ɗan alAswad - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi idan ya gamu da wani mutum daga kafirai a yaƙi, sai suka yi fito na fito da takubba, har kafirin ya samu ɗaya daga hannayen sa da takobi sai ya yanke shi, sannan kafirin ya gudu daga gare shi ya katangantu da wata bishiya, sai ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shin ya halatta a gareni in kashe shi bayan ya yanke hannuna? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: Kada ka kashe shi. Sai ya ce ya Manzon Allah, lallai cewa shi ya yanke ɗayan hannayena, shin a tare da hakan ba zan kashe shi ba? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ka kashe shi, domin cewa shi ya wayi gari jininsa haramun ne, domin cewa kai in ka kashe shi bayan musuluntarsa; to cewa shi a matsayinka ne wanda jininsa abin tsarewa ne da musuluntarsa, kuma kai kana matsayinsa abin halaratawar jini da ka kashe shi dan yin ƙisasi.