explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwadayin musulmi akan aikata farillai da barin abubuwan da aka haramta, da kuma manufarsa ta zama shiga Aljanna.
  • Muhimmancin aikata halal da kudirce halaccinsa, da kuma haramta haram da kudirce haramcin shi.
  • Aikata wajibai da barin abubuwan da aka haramta, sababi ne na shiga Aljanna.