Wasu mutane daga mushrikai sun zo wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sun kasance haƙiƙa sun yawaita kisa da zina, sai suka cewa Annabi: Lallai abin da kake kira zuwa gareshi na musulunci da koyarwarsa abu ne mai kyau, sai dai halimmu da abin da muka afka a cikinsa na shirka da manyan zunubai, shin akwai kaffara a ciki? Sai ayoyi biyu suka sauka: Yayin da Allah Ya karɓi tuba daga mutane tare da yawan zunubansu da girmansu, da ba don haka ba, da sun zarce a kan kafircinsu da shisshiginsu da kuma ba su shiga wannan addinin ba.