Anas dan Malik - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin cewa: Lokacin da sahabbai suna zaune tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikin masallaci yayin da wani mutum ya shigo akan wani rakumi, sai ya durkusar da rakumin sannan ya daure shi. Sannan ya tambayesu: Waye Muhammd a cikinku? Alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kishingide tsakanin mutanen, sai muka ce : Wannan farin mutumin. Sai mutumin ya ce da shi: Yakai Dan Abdul Muddalib. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce da shi: Na ji ka yi tambaya in amsa maka. Sai mutumin ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ni mai tambayarka ne kuma mai tsananta maka a tambaya, kada ka ji wani abu game dani a ranka. Wato: Kada ka yi fushi da ni kuma kada kunci ya sameka. Sai ya ce: Ka tambayi abinda kake so. Sai ya ce: Ina ina hada ka da Ubangijinka kuma Ubangijin wadanda suka gabace ka, shin Allah ne Ya aikoka zuwa ga mutane? Sai ya ce: Eh ya Allah, dan karfafa gaskiyarsa. Sai Mutumin ya ce: Ina yi maka magiya da Allah, wato; Ina tambayarka sabo da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da ka yi salloli biyar a yini da dare? Su ne salloli wadanda aka faralanta ?., Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka da mu azimci wannan watan daga shekara? wato: Watan Ramadan, Ya ce: Eh ya Allah, Ya ce: Ina maka magiya da Allah, shin Allah ne Ya umarceka daka karbi wannan sadakar daga mawadatanmu sai ka rabata ga talakawanmu? ita ce zakka. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Eh ya Allah, Sai Dimam ya musulunta, kuma ya ba Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - labarin cewa shi zai kira mutanensa zuwa Musulunci. Sannan ya yi bayanin kansa cewa shi ne Dimam dan Sa'alabata daga Banu Sa'ad Ibnu Bakar.