Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa Za’a zo da mutuwa ranar Alkiyama, kamar siffar namijin tinkiya a jikinsa akwai fari da baki, Sai a yi kira: Ya ku 'yan Aljanna! sai su dago wuyan su da kawunansu suna dubawa. Sai ya ce da su: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun ganta sun kuma santa, Sannan mai kira ya yi kira: Ya ku 'yan wuta, sai su dago wuyansu su dago kawunansu suna dubawa. Sai ya ce: Shin kun san wannan?. Sai su ce: Eh, wannan mutuwa ce, kuma dukkaninsu hakika sun gan ta. Sai a yankata, sannan mai kira ya ce: Ya ku 'yan Aljanna wanzuwa har abada babu mutuwa,m. Ya ku 'yan wuta wanzuwa har abada babu mutuwa. Wannan dan ya zama kari a cikin ni'imar muminai, da masifa a cikin azabar kafirai. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta: {Kuma ka yi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin rafkana, kuma ba su yin imani ba.} Ranar Alkiyama za'a rabe tsakanin 'yan Aljanna da 'yan wuta, kuma kowanne zai shiga inda zai dawwama a cikinsa. Sai mai munanawa ya yi nadama dan bai kyautata ba, mai takaitawa kuma dan bai kara alheri ba.