Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a cikin aljanna akwai wani wurin da zasu dinga taruwa a wurin, babu siye da siyarwa a cikinsa suna ɗaukar abinda suke so daga gare shi, suna zuwa wurin gwargwdan kwana bakwai, sai iskar arewa ta taso, sai ta motsa a fuskokinsu da tufafinsu, sai su ƙara kyau da ƙawa, sai su koma zuwa ga iyalansu alhali haƙiƙa sun ƙara kyau da ƙawa, sai iyalansu su ce musu: Wallahi haƙiƙa a bayanmu kun ƙara kyau da ƙawa, sai su ce: Kuma wallahi haƙiƙa kun ƙara kyau da ƙawa a bayanmu.