Ankarbo daga Abu Sa'id -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai 'yan Al-janna suna gano Xakunan waxanda suke samansu kamar yadda kuke ganin Tauraro mai haske da ya wuce a sararin sama daga Gabas ko kuma Yamma don fifikon da ke tsakaninsu" Ingantacce ne - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi