Wani abu ya kai ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sahabbansa, cewa su sun yawaita masa tambaya, sai ya yi fushi ya yi huɗuba sai ya ce: An bijiron da aljanna da wuta; ban taɓa ganin mafi alheri a cikin aljanna daga abinda na gan shi a yau ba. Haka (bantaɓa ganin) mafi sharri mafi yawa daga abinda na gan shi a cikin wuta a yau ba, da kun ga abinda na gani, kuma kun san abinda na sani daga abinda na gan shi a yau da kafin yau da kun ji tsoro, tsoro mai yawa, da dariyarku ta ƙaranta, kuma kukanku ya yawaita. Anas - Allah Ya yarda da shi -: Wani yini bai taɓa zo wa sahabbansa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba - mafi tsanani daga wannan yinin ba, sai suka rufe kawunansu alhali gunji na kuka yana fita daga hanci saboda tsananin kuka. Sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya miƙe sai ya ce: "Mun yarda da Allah a matsayin Ubangiji, da musulunci a matsayin addini, da (Annabi) Muhammad a matsayin annabi". Ya ce: Sai wancan mutumin ya miƙe, sai ya ce: Waye babana? Ya ce: "Babanka shi ne wane". sai (aya) ta sauka: {Yaku waɗanda suka yi imani kada ku yi tambaya game da wasu abubuwa idan suka bayyana gareku zasu munana muku}. [al-Maa'ida: 101].