Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah - Maɗaukakin sarki - zai cewa 'yan aljanna alhali su suna cikinta: Yaku 'yan aljanna, sai su amsa maSa suna masu cewa: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, Sai Ya ce musu: Shin kun yarda? sai su ce: Eh mun yarda; Danme ba zamu yardaba alhali ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarka ba! Tsarki ya tabbatar maSa Zaice: Shin ba zan baku mafifici daga hakan ba? Sai su ce: Wane abu ne mafifici daga hakan?! Sai ya ce: Zan saukar muku dawwamammiyar yarda ta; ba zan yi fushi daku a abayanta ba har abada.