Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da sashin ni'imar aljanna, kuma lallai cewa mumini a cikin aljanna yana da wata shema mai girma mai yalwar ciki, ta gwal ɗaya wacce a cikinta akwai ƙofa, faɗinta da tsawonta a cikin sama mil sittin ne, a cikin kowane ɓangare da nahiya da kusurwarta daga cikin kusurwoyin ta huɗu akwai mata, sashinsu ba ya ganin sashi, mumini zai kewayesu.