An cewa Usama ɗan Zaid Allah - Ya yarda da su - Shin baka shiga wurin Usman ɗan Affan - Allah Ya yarda da shi - ba ka yi masa magana cikin abinda yake faruwa na fitina tsakanin mutane da kokari a kasheta gabaɗayanta, sai ya sananar da su cewa shi ya yi masa magana a sirri dan neman maslaha badan tada fitina ba, manufarsa cewa shi ba ya son bayyanar da inkari ga sarakuna a cikin jama'a, sai ya zama sababi na rena khalifa, kuma shi ne kofar fitina da sharri ba zan zama farkon wanda zai buɗeta ba. Sannan Usama - Allah Ya yarda da su - ya ce: Shi yana yi wa sarakuna nasiha a boye kuma ba ya yi wa wani mujamala koda sarki ne, kuma ba ya yi musu fadanci sai ya yabe su a gabansu da karya, hakan bayan ya ji daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi za’a zo da wani mutum ranar alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin (kayan) cikinsa su fito daga cikinsa da gaggawa saboda tsananin zafi da tsananin azaba, sai ya kewaya da 'ya'yan cikinsa yana wannan halin kamar kewayawar jaki a gefan dutsen nikansa, sai 'yan wuta su taru a gefansa kamar sarkar data kewaye shi, sai su tambaye shi : Ya wane, shin ba kaine ka kasance kana umartarmu da aikin alheri ba kuma kake hanamu abin ki ba?! Sai ya ce: Lallai ni na kasance ina horo da aikin alheri amma bana aikata shi, kuma ina hani daga abin ki kuma ina aikata shi.