Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana haƙiƙanin gibar da aka haramta, ita ce: Ambaton musulmi mai gibar da abin da yake ki, daidai ne ya kasance daga siffofinsa ne na halitta ko na ɗabi'a, kamar: Mai ido ɗaya mai yawan algus maƙaryaci, da makamancin hakan daga siffofin zargi, ko da waɗannan siffofin sun kasance samammu ne a gareshi. Amma idan babu siffar a tare da shi, to, wannan ya fi tsanani daga giba, shi ne ƙirƙirar ƙarya, wato: Ƙirkirar abin da babu a tare da shi.