explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa bai zamo daga sha'anin mumimi mai cikakken imani ya zama mai yawan aibata mutane a cikin dangantakar su ba, kuma ba mai yawan zagi da tsinuwa bane, kuma ba mai yawan alfasha ne da aiki ko magana wacce babu kunya a cikinta ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kore imani a cikin nassosin shari'a ba ya kasancewa sai dan aikata wani aiki na haramun ko barin wajibi.
  • Kwaɗaitarwa akan kiyaye gaɓɓai da kiyayesu daga munanan abubuwa, musamman ma harshe.
  • Assindi ya ce: A cikin sigar mubalaga a cikin (mai yawan suka, da mai yawan tsinuwa) akwai nuni akan cewa idan suka da tsinuwa sun zama kadan ne ga wanda yake cancantar hakan ba ya cutarwa a cikin siffantuwa da siffofin ma'abota imani.