A zamanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akwai wani mutum sunansa Abdullahi, ana yi masa laƙabi da jaki, ya kasance yana sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - dariya a cikin wasu daga cikin kalamansa, (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance ya yi masa bulala saboda giya, sai wata rana aka zo da shi ya sha giya sai ya sa aka yi masa bulala. Sai wani daga cikin mahalarta ya zage shi, ya ce: Allah Ya tsine masa, ya mamakin yawan zuwan da ake yi da shi ya sha giya?! sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Kada ku yi masa mummunar addu'ar korewa daga rahamar Allah, na rantsae da Allah ban san wani abuba daga gare shi sai cewa shi yana son Allah da ManzonSa.