Hisham Ibnu Hakim Ibnu Hizam - Allah Ya yarda da su - ya wuce wasu manoma daga baubayi a Sham, an tsayar da su a zafin rana, sai ya yi tambaya game da lamarinsu? Sai aka ba shi labarin cewa su an aikata musu haka ne saboda basu bada (jizya ba) alhali su suna da ikon hakan. Sai Hisham - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ina shaida cewa na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai Allah Yana azabtar da waɗanda suke azabtar da mutane a duniya akan zalinci ba tare da wani haƙƙi ba.