Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wuce wasu kaburbura biyu sai ya ce: Lallai masu kaburburan nan biyu ana musu azaba; kuma ba'a yi musu azaba dan wani babban laifi ku a ganinku ba, duk da yake mai girma ne a wurin Allah, amma dayansu ya kasance ba ya himmantuwa da kiyaye jikinsa da tufafinsa daga fitsari har sai ya biya bukatarsa, dayan kuma ya kasance yana tafiya da annamimanci a tsakanin mutane, sai ya dakko zancen wani da nufin cutarwa da sanya sabani da fitina a tsakanin mutane.