Duk abin da masu zage zagen sukai Musaya, zunubin hakan yana kan wanda ya fara su; Saboda shi mai zalunci ne ta hanyar aikinsa, alhali kuwa dayan ba lallai bane ya aikata shi; Saboda yana da izini ya mayar da martani ga wadanda suka zalunce shi, idan wanda aka zalunta ya afkawa Azzalumi ta hanyar wuce iyaka da aka ba shi, to zunubin wanda aka zalunta ya zama ya fi na wanda ya fara shi