explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa lallai Iblis ya yanke ƙaunar muminai masu sallah su dawo bautarsa da yi wa gunki sujjada a cikin tsibirin larabawa, sai dai cewa shi bai gusheba yana kwaɗayi, kuma bai gusheba ƙoƙarinsa da wahalarsa da tafiyarsa ba ta gushe ba a cusa rigingimu a zukatansu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu da makancin wannan a tsakaninsu.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bautar Shaiɗan (ita ce ) bautar gunki; domin cewa shi ne mai umarni da ita kuma mai kira zuwa gareta, saboda dalilin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki - game da (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi -: (Ya babana kada ka bautawa Shaiɗan...).
  • Shaiɗan yana iya ƙoƙari a afkar da rigingimu da gaba da yaƙe-yaƙe da fitintinu tsakanin musulmai.
  • Daga fa'idojin sallah a Musulunci cewa ita tana tsare soyayya tsakanin musulmai, kuma tana ƙarfafa alaƙar 'yan uwantaka tsakaninsu.
  • Sallah ita ce mafi girman alamomin Addini bayan shaida biyu, saboda haka ne aka saki sunan musulmai (da) masu sallah.
  • Tsibirin Larabawa yana da wasu keɓantattun abubuwa banda waninsa cikin garuruwa.
  • Idan an ce haƙiƙa bautar gumaka ta faru a wasu daga sashin tsibirin Larabawa, alhali Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: (Lallai Shaiɗan ya yanke ƙaunar cewa masu sallah su bauta masa...), to wannan labartawa ne game da abinda ya afku a cikin ran Shaiɗan na yanke ƙauna saboda abinda ya gani na nasarori, da shigar mutane a cikin Addinin Allah jama'a - jama'a, hadisin ya labarta ne game da zatan Shaiɗan da abinda yake sa ran zai afku, sannan waƙi'i (ya zama) saɓanin hakan dan wata hikimar da Allah - Mai girma da ɗaukaka - yake nufinta.