Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da sabubban tsirar mumini a duniya da lahira? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Na horeka da al'amura uku: Na farko: Ka kiyaye harshenka daga abinda babu alheri a cikinsa, daga faɗar kowane sharri, kuma kada ka yi wani furuci sai da alheri. Na biyu: Ka lazimci gidanka dan ka bautawa Allah a cikin kaɗaitakarka, ka shagalta da biyayya ga Allah - Mai girma da ɗaukaka -, ka nisanci fitinu a cikin gidanka. Na uku: Ka yi kuka ka yi nadama ka tuba daga abinda ka aikata na zunubai.