Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe bayan ya jefe Ma'izu ɗan Malik al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - haddin zina, sai ya yi wa mutane huɗuba kuma ya ce: Ku nisanci waɗannan ƙazantar da abinda yake muni saboda saɓon da Allah ya hana aikatasu, wanda ya faɗa kuma ya aikata wani abu daga cikinsu to abubuwa biyu sun wajaba a kansa: Na farko: Ya suturta inda Allah Ya suturta shi kada ya bayar da labarin saɓonsa. Na biyu: Ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah kuma kada ya nace a kansu, wanda saɓonsa ya bayyana garemu zamu tsayar masa da haddin da aka ambata a cikin Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan saɓon.