Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Allah - Maɗaukakin sarki - Yana karɓar tuba daga bayinSa. Idan bawa ya yi laifi da rana kuma ya tuba da daddare Allah Zai karbi tubansa, idan ya yi laifi da daddare ya kuma tuba da rana Allah Zai karɓi tubansa. Kuma tsarki ya tabbatar maSa Yana shinfiɗa hannunSa dan tuba dan farin ciki da tuban, da kuma karɓar tuban, ƙofar tuba tana nan a bude har sai rana ta ɓullo daga yammacinta dan alamtar wa da ƙarewar duniya, idan ta ɓullo to za'a kulle ƙofar tuba.