Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani bawa da zai yi zunubi, sai ya kyautata alwala, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu da niyyar tuba daga zunubinsa wannan, sannan ya nemi gafar Allah, sai Allah Ya gafarta masa. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta fadinsa - Madaukakin sarki -: {Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane}. [Aal- Imran: 135].