Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya faɗa a cikin hadisi Kudisi: Ya kai ɗan Adam muddin dai kana roƙoNa kana kwaɗayin rahamata, ba ka yanke ƙauna ba; zan suturta zunubanka zan shafesu batare da kulawa ba a cikinsu; koda wannan zunubin da sabon sun kasance daga manyan zunubai ne. Ya kai ɗan Adam ! Da zunubanka sun yawaita yawan da zasu cika abinda ke tsakanin sama da ƙasa ta inda suka kai sasanninta kuma suka game gefanta, sannan ka nemi gafarata; zan shafe zan gafarta maka dukkaninsu ba tare da kulawa da yawansu ba. Ya kai ɗan Adam: Lallai kai da zaka zo min bayan mutuwa da zunubai da sabo cikin ƙasa, kuma ka zama mai tauhidi baka taranya wani abu daNi ba; dana fuskanci waɗannan zunuban da sabon da gafara cikin ƙasa; domin cewa Ni Mai yalwar gafar ne, kuma ina gafarta dukkan zunubai in banda shirka.