Ubada ɗan Samit - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, kuma ya kasance yana daga waɗanda suka halarci yaƙin Badr babba, kuma shi ne jagoran mutanensa waɗanda suka gabato dan yin caffa don taimakon Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a daren Aƙaba wacce ke Mina - a lokacin da Manzo ya kasance a Makka kafin Hijirarsa zuwa Madina - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana zaune tsakanin sahabbansa sai ya nemi su yi masa alƙawari akan wasu al'amura: Na farko: Kada su taranya wani abu da Allah a bautar Allah ko da ya ƙaranta. Na biyu: Kada su yi sata. Na uku: Kada su aikata zina. Na huɗu: Kada su kashe 'ya'yansu; mazansu dan jin tsoron talauci ko matansu dan jin tsoron aibi. Na biyar: Kada su yi ƙaryar da zasu ƙirƙireta tsakanin hannayensu da ƙafafuwansu inda mafi yawancin ayyuka suna afkuwa ne ta su koda ragowar gaɓɓai sun yi tarayya da su (a ciki). Na shida: Ba za su saɓawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ba a cikin wani aikin alheri. Wanda ya tabbata a cikinsu akan alƙawarin kuma ya lazimci hakan to ladansa yana ga Allah, wanda kuma ya aikata wani abu daga abinda aka ambata - banda shirka - sai aka yi masa uƙuba saboda shi a duniya ta hanyar tsaida haddi a kansa to shi kaffara ne gare shi kuma da shi ne zunubi ya saraya, kuma wanda ya aikata wani abu sannan Allah Ya suturta shi to al'amarinsa yana ga Allah; idan Ya so zai yi masa afuwa idan kuma Ya so zai yi masa uƙuba, sai duk waɗanda ke gurin suka yi masa caffa (mubaya’a) akan hakan.