Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi mai cikakken Musulunci shi ne wanda musulmai suka kubuta daga harshensa ba ya zaginsu kuma ba ya la'antarsu, ba ya gulmarsu, kuma ba ya tafiya tsakaninsu da kowanne nau'i na nau'ukan cutarwa da harshensa, kuma suka kubuta daga hannunsa ba ya yi musu ta'addanci, ba ya ƙwatar dukiyoyinsu ba tare da wani haƙƙi ba, da makamantan hakan, mai hijira shi ne wanda ya bar abinda Allah - Madaukakin sarki - Ya haramta.