Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana ba wa sahabbansa labari game da mafi girman zunubai, sai ya ambaci waɗannan ukun: 1. Yi wa Allah shirka: Shi ne juyar da kowanne nau'in ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa. 2. Saɓawa iyaye: Shi ne kowacce irin cutarwa ga iyayen, magana ce ko aiki, da barin kyautatawa musu. 3. Faɗin zur, shaidar zur tana daga ciki: Shi ne dukkanin maganar da take ƙarya ce da aka yi nufin tauye wanda ta faɗa kansa ta hanyar ƙwace dukiyarsa da keta mutuncinsa, ko makamancin hakan. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya maimaita gargaɗi game da faɗin zur don faɗakarwa a kan muninta da mummunan gurbinta ga zamntakewa, har sai da sahabbansa suka ce: Ina ma dai ya yi shiru don tausaya masa, da kuma ƙin abin da zai tayar masa da hankali.