Cikin wannan Hadisi akwai tsawatarwa mai tsananani daga Karya da kuma Narko ga wanda yake Karya saboda Raha da sanya Mutane dariya, saboda haka ya Zamanto mafi Munin Masu Muni, Kuma aka girmama Haramcinsa, to wannan yana daga cikin Munanan Halayan da suka Wajaba kan Mumini ya tsarkake Kansa daga su, Kuma ya nisanta daga su, kuma ya tsaekake Harshensa cikin kowane Hali daga cikin Halayan da ya samu kansa, sai abunda Shari'a ta yi masa Izini a cikinsa, Kamar yadda yake ya haramta yin zancen Karya saboda Raha kamar yadda ya haramta sauraron ta idan suka san cewa Karyar ce ya Wajaba akansu Inkarinta.