Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa; Salloli biyar ababen faralantawa a yini da dare ne, da sallar Juma'a a kowane mako, da azimin watan Ramadan a kowacce shekara, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne na kananan zunubai da sharadin nisantar manyan zunubai. Amma manyan zunubai kamar zina da shan giya ba mai kankaresu sai tuba.