explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa musulmi a bayan idonsa ta hanyar hana zarginsa ko munana masa, to, lallai Allah Zai kareshi daga azaba a ranar al-ƙiyama.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani daga magana a kan mutuncin musulmai.
  • Sakamako yana kasancewa ne daga jinsin aiki, wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kareshi daga wuta.
  • Musulunci addinin 'yan uwantaka ne da taimakekeniya a tsakanin ma'abotansa.