explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya kwaɗaitar a kan aikin alheri, kuma kada ya wulaƙantashi ko da ya kasance kaɗan ne, daga wannan (akwai) sakin fuska ta hanyar murmushi a yayin haɗuwa, to, yana kamata ga musulmi ya yi kwaɗayi a kansa; saboda abin da ke cikinsa na ɗebe kewa ga ɗan uwa musulmi da shigar da farin ciki gareshi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar soyayya a tsakanin muminai da murmushi da walwala a yayin haɗuwa.
  • Cikar wannan shari'ar da tattarowarta, kuma ita ta zo da dukkanin abin da a cikinsa akwai gyara musulmai da haɗe kansu.
  • Kwaɗaitarwa a kan aikata aikin alheri ko da ya ƙaranta.
  • An so shigar da farin ciki ga musulmai; saboda abin da ke cikin hakan na tabbatar da sabo a tsakaninsu.