Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u». Tirmizi ya ce Hadisi ne Hasan - Tirmizi ne ya ruwaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga bayi a kan rahamarSa da gafararSa da kuma rangwaminSa.
  • Hadisin ya ƙunshi haƙƙoƙi uku: Haƙƙin Allah da taƙawa, da haƙƙin rai ta hanyar aikata kyawawan halaye bayan munanan (halaye), da kuma haƙƙin mu'amala ta hanyar aikata kyawawan ɗabi'u.
  • Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan (halaye) bayan munanan (halaye), da kyawawan ɗabi'u, na ɗabi'un tsoron Allah, kawai an ambace su da ambato ne dan buƙatuwa zuwa ga bayaninsu.