Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda a al'adarsa ba ya godewa mutane akan alheri da abu mai kyau da suka yi masa to ba zai godewa Allah ba, hakan dan haduwar al'amura biyun da ɗaya, domin wanda daga cikin ɗabi'arsa da al'adarsa ita ce butulcewa ni'imar mutane da barin gode musu, to al'adarsa zata zama butulcewa ni'imar Allah da kuma kasawa a gode maSa.