Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da gaskiya, kuma ya bada labarin cewa lazimtarta yana kaiwa zuwa aiki na gari madawwami, mai lazimtar aikin alheri yana kai mai shi zuwa ga aljanna, ba zai gushe ba gaskiya tana mai maituwa ga reshi a boye da fili, kuma yana cancantar sunan mai yawan gaskiya; shi ne kai matuƙa a gaskiya, Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya tsawatar daga ƙarya da faɗar ƙarya; domin cewa ita tana kaiwa zuwa karkacewa daga daidai da kuma aikin sharri da ɓarna da saɓo, sannan ta kaishi zuwa wuta, ba zai gusheba yana yawaita ƙarya har sai an rubuta shi cikin maƙaryata a gurin Allah.