Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitawa uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - sauƙi, kuma Allah Mai sauƙi ne Mai sauƙaƙawa bayinSa ne, yana son sauƙi garesu ba Ya so musu tsanani, dan haka ba Ya ɗora musu abinda yafi ƙarfinsu, kuma Yana son bawanSa ya siffantu da tausayi a lamura da kuma riƙo da sauƙi; kada ya zama mai kaushin zuciya mai tsanantawa, kuma cewa Allah - Maɗaukakin sarki - a duniya Yana bada kyakkyawan yabo da samun abin nema da sauƙaƙa abin nufi saboda sauƙi da tausasawa, a lahira kuma Yana bada gwaggwaɓan lada, sama da yadda Yake bayarwa akan tsanani da kausasawa, sauƙi yana zuwa tare da abinda waninsa ba ya zuwa tare da shi.