An rawaito daga Jabir Allah ya hyarda da shi daga Annabi cewa shi idan yayi niyyar yaki sai ya ce: "Ya ku Jama'ar Muhajirai da Mutanen Madina, Lallai cewa daga cikin ku akwai wasu Mutane basu da Dukiya, ko Dangi, saboda haka wani daga cikinku ya hadu da Biyu ko Uku"
Ingantacce ne - Abu Daud Ya Rawaito shi
Ma'ana: Cewa Annabi ya Umarci Sahabbansa -Allah ya yarda da su- cewa Mutane biyu ko Uku suna Musanyen rakumi daya har sai ya kasance baki dayansu dai dai