An tambayi annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da aikin da zai zama sababin shiga aljanna, ko game da mafi soyuwar ayyuka a wurin Allah? Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce wa mai tambayar: Ka lazimci yawan sujjada a cikin sallah, domin kai ba za ka yi wa Allah sujjada ba sai Ya ɗaga darajarka da ita, kuma Ya kankare kurakuranka da ita.