Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu wani musulmin da lokacin sallar farilla zai shigo masa, sai ya kyautata alwalarta, ya cikata, sannan ya yi khushu'i a sallarsa ta inda zuciyarsa da gabbansa gaba dayansu zasu zama masu fuskantar Allah masu halarto girmansa, kuma ya cika ayyukan sallah kamar ruku'u da sujjada da waninsa, sai ta zama mai kankarewa ce ga abinda ke gabanta na kananan zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi daga manyan laifuka ba, wannan falalar mai mikewa ce iya shudewar zamani kuma a kowacce sallah.