explain-icon

Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Babu wani ɗaya wanda ya sallaci sallar Asuba, da sallar La'asar kuma ya dawwama a kansu da zai shiga wuta; ya keɓanci waɗannan salloli biyun; domin cewa su ne mafi nauyin salloli, kuma cewa lokacin safiya yana kasancewa ne lokacin bacci da daɗinsa, lokacin La'asar kuma yana kasancewa ne a lokacin shagaltuwa da ayyukan yini da kuma kasuwancinsa, wanda ya kiyaye akan waɗannan salloli biyun tare da samun wahala to zai kiyaye akan ragowar sallolin.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar salloli biyu Asuba da La'asar, to kiyayewa akansu yana wajaba.
  • Wanda ya yi waɗannan sallolin zai zama galibi ba shi da kasalar zuciya da kuma riya, kuma mai son ibada.