explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa wanda ya sallaci Asuba, to, zai kasance cikin kiyayewar Allah da gadinsa da tsarinsa, kuma Zai yi kariya gareshi, kuma zai yi ɗauki gareshi. Sannan (Annabi) tsira da aminci su tabbata a gareshi ya yi gargaɗi game da warware wannan alƙawarin da ɓatashi, ko dai da barin sallar Asuba, ko da bijirowa mai sallatarta da ta'addanci a kansa, to, duk wanda ya aikata haka to haƙiƙa ya keta wannan tsarin, kuma ya cancanci narko mai tsanani na cewa Allah Zai nemeshi saboda abin da ya yi sakaci na haƙƙinsa, wanda kuwa Allah Ya nemeshi Zai kamashi, sannan Ya jefashi a wuta ta fuskarsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin muhimmancin (sallar) Asuba da falalarta.
  • Gargaɗi mai tsanani game da bijirowa da mummunan (aiki) ga wanda ya sallaci Asuba.
  • Kamun Allah - Maɗaukakin sarki - ga wanda yake bijirowa bayinsa na gari.