Daga Abu Huraira Allah ya yarda da shi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Shin kuna ganin cewa da ace akwai wata korama a kofar dayanku yana wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, shin kuna zatan wani abu na dattinsa zai rage ?" Suka ce: Ba abin da zai rage dattinsa, ya ce: "To hakan tamkar salloli biyar ne, Allah Yana shafe kurakurai da su". Ingantacce ne - Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kamanta salloli biyar a kowanne yini da dare a kawarwa da kankarewarsu ga kananan zunubai da kurakurai da korama a kofar mutum da yake wanka a cikinta kowacce rana sau biyar, babu wani abu da zai ragu daga dattinsa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Wannan falalar ta kebanci kankare kananun zunubai ne, amma manya babu makawa daga tuba daga gare su.
  • Falalar yin salloli biyar da kiyayewa akansu da sharuddansu da rukunansu da wajibansu da sunnoninsu.