Wani mutum daga sahabbai ya ce: Ina ma na yi sallah in huta, kai ka ce waɗanda ke gefensa sun aibata hakan gare shi , sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Ya kai Bilal! ka kira sallah ka yi iƙamarta; don mu samu hutu da ita; saboda abin da ke cikinta na ganawa da Allah - Maɗaukakin sarki - da kuma hutu ga rai da zuciya.