Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ba da labari game da munafukai da kasalarsu a kan zuwa sallah, musamman ma sallar Issha'i da Asuba, kuma cewa su da ace suna sanin girman lada da sakamako a halartarsu tare da jama'ar musulmai da sun zo musu ko da da rarrafe ne kamar rarrafen yaro da hannaye da kuma gwiwoyi. Haƙiƙa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi niyyar ya yi umarni a tsai da Sallah, sai ya sanya wani mutumin ya yi wa mutane limanci a maimakonsa, sannan ya tafi tare da shi akwai wanda zai ɗauki ɗauri na itatuwa zuwa mazajen da ba sa zuwa sallar jama'a, sai ya ƙona gidajensu da wuta; sabo da tsananin abin da suka aikata na laifi a hakan, - sai dai bai aikata ba - sabo da abinda ke cikin gidaje na mata da yara da babu-ruwansu da kuma wasunsu cikin masu uzuri waɗanda ba su da wani laifi.