explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga riƙon gona; domin hakan yana daga sabubban kwaɗayi a duniya da karkata zuwa gareta abar lahira.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Hani akan yawaita neman duniya da abinda yake kaiwa zuwa juyawa lahira baya.
  • A cikin hadisin babu hani daga riƙon binda yake akwai abin samun rayuwa daga gare shi, kaɗai hani ne daga dulmiya a cikin duniya da kuma mantawa da lahira.
  • Sindi ya ce: Abin nufi: Kada ku zirfafa a cikin riƙon gona sai ku shagalta da ita daga ambatan Allah.